Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano (KSBS) ta nesanta kanta da wani rahoto da aka wallafa wanda ke dauke da alkalumma kan yawan jama’ar jihar, masana’antu, masallatai, coci-coci da kuma yawan yara kanana da ake zargi suna yawo a kan tituna ba tare da iyaye ba. Ta bayyana wadannan ikirari a matsayin mai rudarwa kuma mara tushe.
Babban Daraktan Hukumar, Dr. Suraj Sulaiman ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, yana mai cewa rahoton, wanda aka danganta ga wani mutum mai suna Garba Adamu kuma wata kafar yada labaran yanar gizo mai suna “The Sultan of Hausa Land” ta yada, ba ya dauke da alkalumman hukuma da hukumar ta fitar.
Hukumar ta ce alkalumman da ke cikin rahoton ba daga gare ta suka fito ba, kuma ba su nuna gaskiyar binciken kididdigar hukumar ba.
“Ikirarin da mawallafin ya yi na cewa Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano ce ta samar da bayanan, gaba daya karya ne, an yi ne domin rudarwa, kuma ba shi da wani tushe balle makama.”
Yayin da take bayyana bayanan da take da su sahihai, hukumar ta ce yawan masana’antu dake aiki a Jihar Kano, wadanda suka hada da kananan masana’antu, matsakaita da manya, a halin yanzu sun kai 3,632, sabanin masana’antu 58 da rahoton ya yi ikirari.
Hukumar ta bayyana cewa wannan adadi ya ginu ne a kan sahihin kidayar masana’antu da hukumar KANINVEST ta gudanar tare da hadin gwiwar KSBS.
Haka kuma, ta yi watsi da ikirarin cewa Jihar Kano tana da masallatai 435,389, inda ta ce bayanan hukumar na gaskiya sun nuna cewa masallatan Juma’a 2,333 ne kacal a jihar.
“Haka zalika, rahoton bai kawo wata cikakkiyar shaida ba game da ikirarin da ya yi na yawan coci-coci.”
Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano ta kuma musanta ikirarin cewa akwai yara kanana miliyan 3.67 marasa iyaye da ke yawo a titunan Kano. Ta bayyana adadin a matsayin na kanzon kurege, wuce gona da irj, kuma babu alkalumman hukuma da suka goyi bayansa.
A cewar hukumar, wani sahihin bincike da aka gudanar ya gano mabarata 6,573 a kan tituna, daga cikinsu 457 kacal, wato kashi 7 cikin 100 ne ke da shekaru tsakanin haihuwa zuwa goma.
Saboda haka, hukumar ta kalubalanci mawallafin da ya bayyana hanyoyin bincike, majiyar bayanai, da shaidun da ya yi amfani da su wajen fitar da wadannan alkalumma da ake takaddama a kai.
Ta kuma tunatar da daidaikun mutane, kungiyoyi, cibiyoyin bincike, da abokan hulda na ci gaba cewa, wajibi ne a sami izini na musamman da amincewar hukumar KSBS kafin a gudanar da kowane irin binciken kididdiga ko tattara bayanai a Jihar Kano.
Ta jaddada aniyarta na samar da sahihan alkalumma da suka dogaro kan hujjoji domin taimakawa wajen tsara manufofi na gari, ci gaba mai dorewa da kuma tattaunawa ta gari a Jihar Kano.











































