
Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwanin gwamna a jam’iyyar APC a jihar.
Fubara ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Laraba, yana mai cewa zai goyi bayan duk wanda ya yi nasara a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Gwamnan ya ce yanke shawarar ya biyo bayan tattaunawa mai zurfi da iyalinsa, abokai, da abokan siyasa.
“Bayan yin tunani mai zurfi da tattaunawa sosai da iyalina, abokai, da abokan hulda, na yanke shawara mai wahala amma mai muhimmanci na janye wa daga zaben fidda gwanin gwamna a APC. Na yi haka da zuciya daya kuma da himma ta goyon bayan wanda ya nasara a matsayin dan takar jam’iyyarmu mai albarka.” in ji Fubara.
Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sake daidaitawar siyasa gabanin babban zaɓen 2027 a Jihar Rivers.
Fubara ya ce ko da yake shawarar tana da wahala, a himmace nake wajen goyon bayan wanda zai zama dan takar gwamna a APC.
A cewarsa, shugabanci yana bukatar sadaukarwa, kuma burin mutum wani lokaci dole ne ya ba da hanya ga muradin jama’a baki daya.
“Jihar Rivers ta fi kowane mutum girma, kuma a wannan lokaci mai muhimmanci, zaman lafiya, kwanciyar hankali, da hadin kan jihar mu mai daraja dole ne su zo gaba da kowane muradi na kai,” in ji shi.
Gwamnan ya bayyana godiyarsa ga magoya bayansa bisa amincinsu, addu’o’i da sadaukarwarsu a duk lokacin wannan tafiyar siyasar, inda ya ce da yawa za su ji haushi kan janyewar ta sa.
Idan za a iya tunawa, shugaban APC kuma dan takarar gwamna na 2027 a Jihar Rivers, Tonye Cole, shi ma ya sanar da janyewarsa daga takarar, yana mai cewa yanke shawarar na da dalilai daban-daban, na cikin muradin hadin kan jam’iyyar.











































