Aikin Hajji: Sama da maniyyatan Najeriya dubu 9 aka kai Madina – NAHCON

FB IMG 1778134513451 720x430

Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON) ta ce akalla mutane 9,000 yan Najeriya sun isa birnin Madina domin gudanar da ibadar aikin Hajji na shekarar 2026.

Bisa bayanan da jami’an NAHCON na Saudi Arabia suka bayar, an kai wadannan alhazan ne tun daga ranar Lahadi da aka fara aikin jigilar alhazan ta jirgi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa hukumomin Saudi Arabia sun amince da alhazan Najeriya 50,000 domin su gudanar da aikin Hajji a shekarar 2026.

Ana sa ran alhazan za su kwana hudu a Madina kafin a kai su Makkah.

Bayanan da NAHCON ta fitar sun nuna cewa jirgi na farko ya tashi a ranar Lahadi a jirgin UMZA mai lamba UMZ3501, wanda ya kai alhazan Kogi 473 zuwa Madina, wanda ya kunshi maza 296 da mata 177.

Bayan haka, jirgin Flynas ya kai alhazan Kebbi 418, wadanda suka kunshi maza 259 da mata 159.

Haka kuma jirgin MaxAir ya kai alhazan Nasarawa 560, wadanda suka kunshi maza 381 da mata 179.

A ranar Litinin, jirgin Airpeace ya tashi daga Legas zuwa Madina da alhazan Oyo 315, maza 155 da mata 160.

Jirgin Flynas ma ya tashi daga Kebbi zuwa Madina a ranar Litinin, yana dauke da alhazan Kebbi 427. Sun kunshi maza 283 da mata 144 tare da jami’ai biyu.

Haka kuma jirgin UMZA ya tashi daga Dutse, Jigawa, da alhazan 480, wadanda suka kunshi maza 306 da mata 174.

Sannan jirgin MaxAir ya tashi daga Gombe zuwa Madina da alhazan 411, wadanda suka kunshi maza 238 da mata 173.

NAHCON ta kuma kai alhazan Nasarawa 557, Jigawa 394, karin alhazan Nasarawa 424, Osun 343, da Gombe 550.

An kuma kai alhazan Kebbi, Kwara da Plateau zuwa Madina.

A halin yanzu, Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Yusuf, ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa hukumar ta ci gaba da jajircewa wajen kula da walwala alhazan Najeriya.

Yusuf ya bukaci alhazan da su tabbatar da halayensu a kasa mai tsarki ya kasance cikin tawali’u.

Haka kuma Mataimakin Shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya bukaci alhazan da su rike dabi’u na kasa wadanda ke nuna Najeriya cikin kyakkyawan hali, su kuma zama jakadu nagari na kasar.

Shettima ya bayyana alhazan a matsayin wakilan kasar a duniya wadanda dole ne su nuna nagartar kasar yayin da suke bin dokokin kasar da suke karba.

“Ku jakadu ne na Najeriya, kuna dauke da hoton kasarmu da mutuncin al’ummarmu.

“Bari halayenku su nuna tarbiyya, tawali’u, hakuri, da gaskiya,” in ji shi.

Mataimakin shugaban kasa ya bayyana aikin Hajji a matsayin yarjejeniya tsakanin Najeriya da ‘yan kasa.

Ya ce gwamnati za ta tabbatar da nauyin kula da ‘yan kasa yayin da alhazan ke tabbatar da dabi’u na kasa.

Ya ce aikin Hajji yana dora wa hukumomin gwamnati nauyi na kai tsaye na tabbatar da mutunci, tsaro, da tafiyar da alhazan ba tare da cikas ba.

“Nauyinmu shi ne tabbatar da cewa kowane dan alhaji ya gudanar da wannan tafiya ba tare da wata wahala da ba dole ba, ko tsoro da ba dole ba, ko cikas da za a iya kaucewa ba,” in ji shi. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here