Gwamna Yusuf ya raka Gwarzo wajen karbar katin jam’iyyar APC

IMG 20260506 WA0018 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Mataimakinsa Murtala Sule Garo ya wakilce ta, ya raka Sanata Bello Hayatu Gwarzo domin karbar katin Jam’iyyar APC.

A wani biki na gajeren lokaci da aka gudana a Karamar Hukumar Gwarzo a ranar Talata, lamarin da ya nuna kammala ficewar Sanata Gwarzo zuwa jam’iyyar mai mulki a hukumance.

Taron ya samu halartar mambobin jam’iyyar masu yawa,masu ruwa da tsaki da masu goyon baya daga fadin jihar, wanda yadda jam’iyyar ta APC ke samun karfi a Kano.

Daga cikin manyan baki da suka halarci taron akwai Tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau da Dr Abdullahi Umar Ganduje, Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi T. Gwarzo, Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi; Dan majalisar da ke wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir Koki, Dan majalisar da ke wakiltar Gwarzo/Kabo, Abdullahi Mu’azu Babangandu, Shugaban APC na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, Muntari Ishaq, Sakataren APC, da sauransu.

Da yake jawabi a taron, Murtala Garo ya bayyana shigowar Gwarzo cikin APC a matsayin wani babban abu a siyasa, yana mai cewa tasirinsa da goyon bayansa na matakin kasa za su kara karfafa tsarin jam’iyyar a fadin jihar.

Ya ce, “A madadin Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf, na raka Sanata Bello Hayatu Gwarzo yayin da ya zama mamba mai rijista na babbar jam’iyyarmu, wannan babban ci gaba ne da ke karfafa karfinmu da ke karuwa a fadin jihar.”

Garo ya sake jaddada kudirin gwamnati na “Kano First”, wanda ke da niyyar ba da fifiko ga walwalar jama’a ta hanyar ci gaba da saka hannun jari a ilimi, samar da ruwa, lafiya da noma.

Ya yi kira ga mambobin jam’iyya da masu goyon baya da su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai da kuma bin ka’idodin APC gabanin babban zaben 2027.

Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da mara wa APC baya tare da zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf a 2027 domin tabbatar da ci gaba da karfafa ci gaban da ake samu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here