Gwamnan Yobe ya bai wa daliban da suka samu nasara a gasar Turanci ta duniya da muhawara kyautar naira miliyan 30

FB IMG 1769724164738 750x430 (1)

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya sanar da bayar da kyautar kuɗi har naira miliyan 30 ga daliban nan uku da suka yi fice a fannin harshen Turanci da muhawara a gasar TeenEagle ta duniya ta shekarar 2025 da aka kammala a birnin London.

Ɗalibai mata ukun, wato Nafisa Abdullahi da Ruqayya Fema da Hadiza Kalli, su ne suka zama zakaru gaba ɗaya a gasar, kuma dukkansu ɗalibai ne na Kwalejin Najeriya Tulip ta kasa da kasa da ke Mamudo a jihar.

Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana hakan ne a Damaturu, inda yace, nasarar da suka samu ta ɗaukaka martabar Jihar Yobe da ƙasar Najeriya baki ɗaya a idon duniya.

Ya bayyana cewa kyautar kuɗin da aka bayar na da nufin ƙarfafa gwiwar ɗaliban wajen neman ilimi da kuma nuna ƙwarewa a fagen ilimi da muhawara a matakin ƙasa da na duniya.

Baya ga kyautar kuɗin, gwamnan ya kuma amince da ba wa daliban guraben karatu domin ci gaba da karatu a manyan makarantu, domin su samu damar cimma burinsu na ilimi.

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin Jihar Yobe za ta ci gaba da tallafa wa matasa masu basira da hazaka, tare da samar da yanayi da zai ba su damar yin fice a fannoni daban-daban na rayuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here