Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa reshen jihar Kano ta kama mata biyu da ake zargi da yunkurin shigar da miyagun ƙwayoyi cikin gidan gyaran hali da ke Goron Dutse a Kano.
Wannan na cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, ya fitar, inda ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a yayin ƙoƙarin da hukumar ke yi na hana shigar haramtattun kayayyaki cikin gidajen gyaran hali.
Sanarwar ta bayyana cewa matan sun haɗar da Maryam Ali da Hauwa Musa, masu shekaru tsakanin 19 zuwa 20, kuma ‘yan asalin jihar Kano, an tare su ne a ranar 21 ga watan Disamba, 2025, yayin binciken tsaro na yau da kullum a lokacin da suke ƙoƙarin shiga cikin gidan gyaran halin.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an same su da wasu abubuwa da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne, inda binciken farko ya nuna cewa suna nufin kai wa fursunoni da ke cikin gidan gyaran halin.
Hukumar ta bayyana cewa irin wannan aiki babban take ne ga ƙa’idojin hukumar kula da gidajen gyaran hali, kuma laifi ne a ƙarƙashin dokokin jamhuriyar tarayyar Najeriya.
Bayan kammala kamen, an miƙa matan ga hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakan shari’a da suka dace.
Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa reshen jihar Kano ta sake jaddada ƙudurinta na tabbatar da tsauraran matakan tsaro da ladabi a ciki da wajen gidajen gyaran hali, tare da nuna rashin amincewa da duk wani nau’i na haramtaccen aiki.
Haka kuma ta yi kira ga jama’a da su bi ƙa’idoji da dokokin ziyartar gidajen gyaran hali, tana gargaɗin cewa duk wanda ya karya doka za a hukunta shi bisa tanadin doka.












































