Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umurci a janye dukkan jami’an ‘yan sanda da ke rakiyar ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati domin mayar da su kan aikin tsaro a faɗin ƙasa.
Shugaban ya bayar da wannan umarni ne a zaman majalisar zartarwa ta tarayya da aka gudanar a fadarsa da ke Abuja, inda ya bayyana cewa ya fi son jami’an su yi aikin tsaro na gaskiya maimakon kasancewa a matsayin masu kula da manya.
Ya bukaci babban sufeton ‘yan sanda da ministan harkokin ‘yan sanda su tabbatar da cika wannan umarni, tare da bayanin cewa duk wani jami’i da ke da matsala zai tuntuɓi babban sufeton ‘yan sanda kafin daukar mataki.
Ya ce ma’aikatar cikin gida, tare da hukumar tsaron farin kaya, za su maye guraben da ‘yan sanda za su bari domin kar a bar jama’a cikin yanayi na rashin tsaro.
Karanta: Tinubu ya nemi majalisa ta tabbatar da sunayen kwamishinoni biyu a hukumar NERC
Shugaban ya umurci mai ba da shawara kan harkokin tsaron ƙasa da hukumar tsaro ta DSS da su kara hada bayanan tsaro tare da kafa kwamiti domin sake nazarin tsarin tsaron ƙasar, ganin cewa matsalolin sace mutane da ta’addanci na bukatar karin jami’ai.
Ya kuma bukaci kwamitin tattalin arzikin ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa da su hanzarta aiwatar da tsarin gyaran kiwon dabbobi domin rage rikicin manoma da makiyaya, tare da neman jihohi su samar da wuraren kiwo da za su koma gonakin kiwo na zamani.
Ya jaddada cewa dukkan gyare-gyaren da suka shafi kiwo za su zama bisa tsarin mulki da ke tabbatar da ikon jihohi kan filaye, yana mai cewa ya zama dole a mayar da yankunan rikici zuwa hanyoyin raya tattalin arziki.













































