Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da kuɓutar da ɗalibai 100 da aka yi garkuwa da su a Jihar Niger

Niger School Abduction2

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da kubutar da ɗalibai 100 na makarantar St. Mary’s da ke Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Niger, kamar yadda tashar talabijin ta Channels ta ruwaito.

A ranar 21 ga Nuwamba 2025 ne ’yan bindiga suka kutsa makarantar cikin dare, inda suka isa wurin da misalin ƙarfe 2:00 na safe a kan babura.

Ƴan bindigar sun shiga dakunan kwanan dalibai na makarantar na tsawon awa uku, inda suka yi awon gaba da mutane 315 da suka haɗar da dalibai 303 da malamai 12.

Jami’an tsaro tare da masu farautar gandun daji daga al’umma sun bazu domin bincike a dazuka da yankunan da ke kusa da wurin, inda a rana ta farko dai dalibai 50 sun tsere daga hannun waɗanda suka sace su kuma suka koma gidajensu.

Sai dai har yanzu mutane 265 ciki har da yara 253 da malamai 12 suna ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa.

Gwamnatin tarayya ta kafa tsauraran matakan tsaro na awa 24 tare da kaddamar da aikin sa ido ta sama a sassan jihohin Kwara, Kebbi da Niger.

Karanta: Tinubu ya bai wa jami’an tsaro umurnin mamaye dukkanin dazukan jihohin Kwara, Neja da Kebbi

Shugaba Bola Tinubu ma ya soke tafiye-tafiyen ƙasashen waje da ya shirya domin kula da lamarin.

Hukumomi sun kuma bada umarnin rufe dukkan makarantun Jihar Niger na ɗan lokaci tare da wasu cibiyoyin tarayya da ke yankunan da ke fuskantar barazana.

A baya-bayan nan mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bai wa iyaye da hukumomin makarantar tabbacin cewa yaran da ke hannun masu garkuwa suna cikin koshin lafiya kuma za su dawo nan bada jimawa ba.

Ya ce an ƙara yawan jami’an tsaro a yankin tare da ci gaba da matakan ceto waɗanda ake tsare da su.

A halin yanzu rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnati ta samu nasarar kubutar da yara 100 daga cikin waɗanda aka sace, kuma ƙarin bayani na tafe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here