Auren Gata: Kada ku rika duba wayoyin mazajen ku– Kwankwaso ya shawarci ma’aurata

Mass Wedding new
Mass Wedding new

Sanata Rabi’u Kwankwaso, shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, ya shawarci ma’aurata 1,800 da ke karkashin shirin auren gata da su guji duba wayar ma’zajen su.

Don gujewa duk wani abu da zai kawo rabuwar aure, in ji shi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Kwankwaso ya yi magana ne a wajen liyafar da gwamnatin jihar ta shirya wa ma’auratan a gidan gwamnatin Kano ranar Asabar.

Ya ce duba wayoyin ma’aurata na daya daga cikin abubuwan da ke kawo rabuwar aure, don haka akwai bukatar ma’aurata su guji duk wani abu da zai iya haifar da rikici.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here