Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe wani mai suna Malam Usman Sarki, Hakimin Kauyen Zazzaga da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.
Wani shugaban al’ummar da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai a cewa, ‘yan bindigar da ake zargin sun kaddamar da harin ne a garin Zazzaga da makwabta da daddare a ranar Talata.
Majiyar ta ce an kuma yi garkuwa da wasu manoma da ba a tantance adadinsu ba da suka hada da mata.
A cewar majiyar, “an kai harin ne cikin dare a ranar Talata. Sun harbe Hakimin garin Zazzaga Malam Usman Sarki har lahira tare da yin garkuwa da wasu da dama.