Zaman lafiya ya dawo a ƙauyen Dangoro bayan masu gonaki da gwamnatin jihar Kano sun cimma matsaya

WhatsApp Image 2025 12 07 at 13.34.44 750x430

Zaman da aka yi tsakanin masu gonaki da gwamnatin jihar Kano ya kai ga fahimtar juna kan yadda za a yi amfani da gonakin da ake takaddama a yankin Dangoro na ƙaramar hukumar Kumbotso tsawon lokaci.

Ci gaban ya biyo bayan zaman da kwamishinan harkokin kasa Abduljabbar Umar Garko, ya yi da al’ummar yankin a ranar 27 ga watan Nuwamba.

A baya dai gwamnatin jihar ta sanar da shirinta na mayar da kasuwar ’yan lemo da kasuwar kayan lambu ta Yankaba zuwa yankin Dangoro, lamarin da ya haifar da fargabar rasa filaye a tsakanin mazauna yankin.

Wannan ya jawo neman shiga tsakani da aka yi wa gwamna Abba Kabir Yusuf ba tare da samun gamsasshen mataki ba.

A ranar Asabar shugabannin masu gonaki sun gudanar da taro domin sanar da sauran jama’a matakan da aka dauka bayan zaman su da kwamishinan ƙasa na jihar.

Labari mai alaƙa: Masu Gonaki da Filaye sun gudanar da Sallar Al’ƙunuti kan yunƙurin gwamnati na sake kwace musu kadarori don gina sabuwar kasuwa

Shugaban ƙungiyar masu gonaki, Alhaji Gambo Saminu Adamu, ya bayyana cewa taron ya tabbatar da cewa matsayar da aka cimma tsakaninsu da gwamnati za ta kasance bisa gaskiya da adalci ga kowa.

Ya ce an tsara yadda za a wakilci duk masu filaye da ba su halarta ba, ko kuma su ke zaune a ƙasashen waje domin tabbatar da an kula da muradunsu.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa tsarin rabon filayen zai kasance kashi hamsin ga masu gonaki da kashi hamsin ga gwamnati, tare da tabbatar da cewa kasuwannin da za a kawo yankin za su amfana da al’ummar Dangoro kamar yadda aka tsara.

A gefe guda, wasu sun jaddada bukatar bin tsarin da aka amince da shi ba tare da wani sabani ko kaucewa ka’ida ba, domin tabbatar da adalci ga mazauna yankin da kuma kare filayensu daga duk wata barazana.

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa tsarin rabon filayen zai ba da damar cigaba tare da tabbatar da hakkokin masu gonaki.

Misali, idan mai fili yana da sararin gina shaguna goma, za a raba su hudu da biyar domin gwamnati da shi mai filin bisa tsarin kashi hamsin-hamsin.

A ƙarshe, mazauna yankin sun nuna kwarin gwiwa amma da taka tsantsan, inda suka ce nasarar shirin tana bukatar gaskiya da bayyana dukkan matakai yadda ya dace domin tabbatar da ganin kowa ya amfana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here