Jami’ar Bayero dake Kano (BUK) ta amince da korar dalibai 57 bisa kama su da laifin aikata magudi a jarabawa daban-daban, domin tabbatar da tsare martabar harkokin ilimi a jami’ar.
Haka kuma, majalisar jami’ar ta dakatar da dalibai 8 na ɗan lokaci saboda laifuka masu sauƙi, yayin da dalibai biyu aka wanke su bayan bincike ya tabbatar basu da laifi.
Rahoton kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne a taron majalisar karo na 427 da aka gudanar ranar Laraba, bisa tanade-tanaden dokokin gudanar da jarabawa da ka’idojin jami’ar (GEAR), tare da sauran dokokin da suka shafi ɗaliban digiri da masu digiri na gaba.
Sanarwar ta fito ne daga hannun daraktan hukumar jarabawa, Malam Aminu Wada Kurawa, inda ya yi karin haske kan matakin.
Ya ce, cikin jerin hukunci akwai ɗalibai 57 da aka kora saboda magudi, 8 da aka dakatar daga zangon karatu ɗaya zuwa biyu, biyu da aka wanke daga laifin da ake zarginsu da shi, sannan kuma akwai shari’ar ɗalibi guda ɗaya da aka ɗage domin ci gaba da bincike.
Daliban da aka hukunta sun fito daga manyan sassan jami’ar daban-daban, ciki har da sashin Ilimi, Injiniya, Kiwon Lafiya, kimiyyar zamani da gudanarwa, kimiyyar Muhalli, har ma da sashen Digiri na gaba.
Karin labari: Malala ta ziyarci Najeriya domin ƙarfafa ilimin ƴaƴa mata
Jami’ar ta jaddada matsayarta na rashin lamuntar duk wani nau’in magudi a jarabawa, tana mai cewa hakan na lalata amincin takardar shaidar kammala karatu da martabar jami’a.
Haka kuma, jami’ar ta shawarci ɗalibai da su rika bin ƙa’idojin jami’a, musamman dokokin jarabawa, domin gujewa fadawa cikin irin wannan hukunci a nan gaba. Ta ce duk da tana marawa ɗalibai baya wajen samun nasara a karatunsu, ba za ta yi shakka ba wajen aiwatar da doka kan wanda ya karya ƙa’ida.













































