Masu neman sanin makamar aiki a jaridar PRNigeria sun kai ziyara SolaceBase don samun kwarewar aikin jarida

WhatsApp Image 2025 09 24 at 10.28.54 750x430

Matasa masu koyon aikin jarida na PRNigeria sun kai ziyara ofishin jaridar SolaceBase dake Kano a ranar Talata, domin haɗa abin da suke koya a aji da kuma aikace-aikace na fili a fagen aikin jarida.

Wannan ya kasance wani ɓangare na shirye-shiryen ba da horo ga matasa da PRNigeria ke gudanarwa a manyan birane uku – Kano, Abuja da Ilorin.

Ziyarar ta samu jagorancin Mohammad Dahiru Lawal, kwararren mai binciken labaran bogi da kuma Shugaban Sashen Kirkire-kirkire da Ayyukan Musamman na PRNigeria.

Lawal ya bayyana cewar manufar ita ce a ba wa matasan fahimta ta musamman kan yadda ake gudanar da harkokin jarida, dabarun yada labarai da kuma dabarun ingantaccen aikin jarida.

A cewar Lawal, SolaceBase ta kafa suna a arewacin Najeriya a matsayin ingantacciyar cibiyar watsa labarai, don haka ya dace matasan su sami kwarewa kai tsaye a irin wannan mahalli.

Karin karatu: Mamallakin jaridar PRNigeria ya kai NIPSS ƙara kan janye shi daga samun horon SEC 47 ba bisa ka’ida ba

Ziyaran na cikin shirin PRNigeria Communication Fellowship, wanda aka fara shi a bara domin horas da matasa 10 da aka zaɓa daga fannoni daban-daban na sadarwa.

A yayin ganawar, wanda ya kafa SolaceBase kuma Babban Darakta, Mallam Abdullateef Abubakar Jos, ya yi wa matasan bayani kan yadda ya shiga aikin jarida, kalubalen da ya fuskanta da kuma darussa da ya koya.

Ya ja hankalin su kan muhimmancin gaskiya da daidaito, tare da ƙara da cewa aikin jarida amana ce ta jama’a wadda ke buƙatar sadaukarwa da haƙuri.

Jos ya gargade su da su kasance masu tantancewa kafin su wallafa wani labari, yana mai jaddada cewa a wannan zamani na fasaha, sahihancin labari ya fi saurin yin sa muhimmanci.

Ya kuma yi kira gare su da su kasance masu son koyo a ko da yaushe, tare da yin tambayoyin da suka shafi al’umma domin kare gaskiya da jama’a.

Matasan sun sami damar tattaunawa da sauran ma’aikatan jaridar, ciki har da edita, inda suka koyi tsarin aikin edita da dabarun gudanar da kafar labarai ta zamani. Ɗaya daga cikin mahalarta, Aliyu Yusha’u, ya bayyana farin cikinsa da kwarewar da suka samu daga ziyarar, yana mai cewa horon yana taimaka musu wajen inganta dabarun sadarwa da kuma yadda za su yi tasiri a fagen jarida.

Ya ƙara da cewa ziyarar ta kasance abin tunawa musamman ganin yadda suka koyi abubuwa masu amfani daga tawagar SolaceBase, wanda ya tabbatar musu da muhimmancin sadaukarwa da bin ƙa’idojin aikin jarida domin cimma nasara.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here