Wata Matar aure ta roƙi kotu da kada ta amince da buƙatar mijinta na neman sakinta

Divorce 750x416

Wata matar aure mai suna Fauziya Ibrahim ta roƙi kotun yankin Ilorin a ranar Laraba da kada ta amince da buƙatar mijinta, Hamza Musbau, na raba auren su.

Fauziya ta bayyana a gaban kotun cewa ta shafe shekaru 16 da aure da mijinta, kuma tana son a ci gaba da zaman aure tsakaninsu.

Ta ce ba ta da niyyar ganin auren ya mutu, domin tana daraja zamantakewar da suka yi tsawon lokaci tare.

Tun da farko, mijin nata Musbau ya roƙi kotu ta raba auren ne bisa dalilin cewa ya rasa ƙauna da kuma ƙwazon soyayya daga wajen matarsa.

Alkalin kotun, Mista Toyin Aluko, ya bayyana cewa bisa tanadin Alƙur’ani mai girma, Allah ya ba wa mace damar neman sulhu kamar yadda shari’a ta halatta saki.

Don haka, ya shawarci Fauziya da ta yi iya ƙoƙarinta wajen sasantawa da mijinta tare da warware duk wata matsala da ke tsakaninsu.

Kotun ta ɗaga sauraron shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Oktoba domin samun rahoton sulhu tsakanin ma’auratan.

(NAN).

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here