Wasu malaman addinin Musulunci a jihar Kano sun sami horo na musamman kan tantance sahihancin labarai da kuma ilimin jarida domin su iya yakar labaran karya da yaudara a cikin hudubobinsu da kuma mu’amalarsu da jama’a.
Wannan horo, wanda Alkalanci, wani dandalin tantance gaskiya ya shirya, ya tattaro mambobin Majalisar Ulama da sauran shugabannin addini daga fadin jihar.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa, horon na tsawon kwana biyu ya mai da hankali wajen samar wa da malamai dabaru na gane labaran karya, tabbatar da gaskiya, da kuma kawar da labaran bogi, musamman a kafafen sada zumunta.
Yayin taron, Shugaban Majalisar Ulama a Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya jaddada muhimmancin malaman addini wajen kare gaskiya da hana yaduwar karya.
Labari mai alaƙa: Matasan jaridar PRNigeria sun kai ziyara SolaceBase don samun kwarewar aikin jarida
Ya ce, yaudara da labaran bogi suna haddasa tashin hankali da rarrabuwar kawuna a cikin al’umma, don haka malaman addini ya dace su zama abin koyi wajen yaɗa adalci da gaskiya.
Haka kuma, Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, wanda Bauren Kano, Alhaji Abbas Dalhatu, wanda shi ne Daraktan rukunin tashoshin Freedom Radio ya wakilta, ya gargadi mahalarta su rika tantance duk wani bayani kafin su yada shi.
Ya yi nuni da cewa kafafen sada zumunta suna da karfin tasiri kan tunanin jama’a, inda ya kara da kawo hujja daga Suratul Naml na Alƙur’ani mai girma, lokacin da Annabi Suleiman ya umurci baransa da tsuntsu su tabbatar da rahoton da aka kawo masa game da Sarauniya Bilqis – abin da ya bayyana a matsayin dalilin farko na tantance labari a cikin Musulunci.
A nasa jawabin, Alhassan Bala, wanda ya kafa dandalin Alkalanci a watan Oktoba 2024, ya ce an zabi shugabannin addini domin rawar gani da suke takawa wajen tsara ra’ayin jama’a.
Ya yi nuni da cewa labaran karya na barazana ga zaman lafiya, hadin kai, da amincewar al’umma, don haka akwai nauyi a kan malaman addini wajen tabbatar da gaskiya a duk abin da suke yaɗa wa jama’a.
Mahalarta horon sun sami koyarwa kan hanyoyin amfani da dabaru na tantance bayanai na kan layi da na wajen layi.
Bala ya mika godiya ga Sarkin Kano, Majalisar Ulama, da sauran masu ruwa da tsaki da suka tallafa wajen gudanar da shirin.
NAN













































