Gwamnatin Jihar Bauchi ta kori wasu manyan ma’aikata biyu daga aikin gwamnati bayan an same su da laifin yin zamba cikin takardu.
Wata sanarwa da Saleh Umar, jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Kula da Ma’aikatan Jihar Bauchi (BSCSC), ya fitar a ranar Laraba a Bauchi ta tabbatar da hakan.
A cewar Umar, wadanda abin ya shafa su ne Yusuf Ningi, jami’in gudanarwa, da Suleiman Ahmed, babban jami’in gudanarwa a mataki na ɗaya.
An kori ma’aikatan ne a zama na 35 na hukumar da aka gudanar a ranar Talata.
Ya bayyana cewa bincike ya tabbatar da laifin zamba da suka aikata, wanda ya saba wa dokokin aikin gwamnati na jihar, karkashin sashe na 0327 (ii, iii da vi).
Umar ya ce korar ta fara aiki tun daga ranar 23 ga Satumba, kuma ma’aikatan sun kasance a ofishin Gidan Gwamnati kafin haka.
Karin labari: SSANU da NASU sun tsawaita wa’adin yajin aiki
Shugaban hukumar, Dr Ibrahim Muhammad, ya yi kira ga sauran ma’aikatan gwamnati a jihar da su rika aiki da tsarin doka da ƙa’idojin aikin gwamnati tare da bin umarnin cikin gida da na waje yayin gudanar da ayyukansu.
Ya ce bin doka zai kare ma’aikata daga aikata ayyukan da ba bisa ka’ida ba tare da tabbatar da ingantaccen aiki ba tare da cin hanci ko rashawa ba.
Bugu da ƙari, hukumar ta amince da karin girma ga wasu manyan jami’ai yayin zaman.
An tabbatar da mukamin Darakta ga mutane uku, yayin da aka daga wasu mataimakan daraktoci hudu zuwa matsayin darakta.
Sannan wasu shugabannin ma’aikata guda takwas an daga su zuwa matsayin mataimakan daraktoci.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa, a ranar 11 ga Satumba, hukumar ta kori wani jami’in ilimi saboda laifin cin zarafi ta hanyar fyade.
NAN













































