Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira biliyan 100 kan shirin ciyar da ɗalibai yan Firamare a kasar nan.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu yace an ware Naira biliyan 100 ne a cikin kasafin kuɗin bana domin aiwatar da shirin ciyar da daliban ƙasar nan.
Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake rattaɓa hannu kan dokar kasafin kuɗin shekarar 2024.
Yace tsarin zai ƙarfafa gwiwar Yara wajen halartar makaranta tare da rage karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta.
Karanta wannan: Gwamnatin tarayya ta dakatar da amfani da takardun Jami’o’in Benin da Togo
Shugaban ya ƙara da cewa kasafin kuɗin, zai taimaka wajen rage yawan kashe-kashen kudin ake yi akai-akai, da kuma kara kudaden da ake kashewa na manyan ayyuka.
Karanta wannan: Yan-sanda suna bincike akan sace shugaban karamar hukuma a Nasarawa
A farkon watan Disambar da ya gabata ne Tinubu ya ba da umarnin sake dawo da shirin ciyar da yara ‘yan makaranta tare da ba da umarnin mai da shi zuwa ma’aikatar ilimi, maimakon ma’aikatar jin kai.
Shirin wanda a baya aka dakatar da shi zamanin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yanzu ya koma ƙarƙashin ma’aikatar ilimi, da nufin inganta harkokin koyo.










































