Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wata matashiya yar shekara 25 a kauyen Nadabo da ke karamar hukumar Tafawa Balewa bisa zarginta da kashe mijinta bayan wata takaddama da suka yi a cikin gida.
Ahmed Wakili shi ne mai magana da yawun rundunar, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Bauchi ranar Litinin.
Ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa ma’auratan sun sha fama da matsalolin aure, musamman batun tsare diyar su Salamatu ‘yar shekara shida da suka yi a baya lamarin da ya kara tayar da zaune tsaye a gidan.”
Lamarin dai ya ta’azzara inda aka yi ta cece-ku-ce, matar ta dauki wuka ta kai dakin kwanan su wanda hakan ya haifar da wannan mummunan lamari.
Jami’an ‘yan sanda na hedikwatar tsaro ta Bununu sun yi gaggawar amsa kiran da aka yi musu, inda suka dauki mijin tare da kai shi zuwa Asibitin Cottage da ke Bununu domin samun kulawar gaggawa.
Wakil ya kara da cewa “Duk da kokarin da ma’aikatan lafiya suka yi, mijin ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu.”
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Auwal Musa, ya umurci hukumar binciken manyan laifuka ta jihar da ta gudanar da sahihin bincike tare da daukar matakin doka bisa sakamakon binciken. (NAN)