Ƙungiyar masu kafafen yaɗa Labarai ta ƙasa (SNB) za ta gudanar da taronta na shekara karo na biyu tare da bikin kaddamar da sabbin mambobi a birnin Kano daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Nuwamba, 2025, bayan kaddamar da kwamitin shirye-shirye na cikin gida domin kula da shirin taron.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa kaddamarwar ta samu ne sakamakon ƙoƙarin shugaban kungiyar, Farfesa Umaru A. Pate, da daraktan yada labarai na gwamnan Jihar Kano, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa, waɗanda suka tabbatar da amincewar gwamnatin jihar da ta karɓi bakuncin taron na kasa.
A cikin wani saƙo daga ƙasar Norway, inda yake halartar taron kasa da kasa, Farfesa Pate ya shawarci mambobin kwamitin su yi aiki da jajircewa domin tabbatar da nasarar taron, wanda ya bayyana a matsayin irinsa na farko da za a gudanar a Kano.
Ya bayyana cewa taron zai jawo sama da masu kafafen yaɗa labarai 400 da sabbin mambobi daga cikin gida da wajen ƙasar.
Ya kuma yaba wa gwamnatin Jihar Kano bisa tallafawa harkar kafafen yada labarai da kuma ƙarfafa ingantaccen tsarin yada labarai mai tsafta a Najeriya.
Kwamitin shirye-shiryen na cikin gida na karkashin jagorancin mataimakin shugaban kungiyar na yankin Arewa maso Yamma, Alhaji Ado Saidu Warawa, yayin da babban manajan gidan rediyon Najeriya Pyramid FM Kano, Dakta Garba Ubale Danbatta, ke matsayin sakatare.
Sauran mambobin sun haɗa da Farfesa Sulaiman Yar’Adua, Farfesa Nura Ibrahim, Farfesa Sule Y. Sule, Hajiya Sa’a Ibrahim (tsohuwar shugabar hukumar BON), Hajiya Wasila Ladan (sakatariyar ƙasa ta kungiyar NAWOJ), Alhaji Sulaiman Dederi (shugaban ƙungiyar NUJ reshen Kano), Ibrahim Y. Dawakin Tofa, Hajiya Aishatu Sule, Muhammad Sunusi Jibrin (babban manajan rediyon AMASCO), da Hajiya Aishatu Bello Mahmud (Freedom Radio Kano).
Bayan kaddamarwar, Alhaji Ado Saidu Warawa ya nuna godiya ga shugabannin ƙasa na kungiyar bisa amincewar da suka nuna wa kwamitin, inda ya tabbatar da cewa za su yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar taron da ke tafe.













































