Majalisar Dattawa ta karɓi rahoton wucin gadi daga kwamitinta na musamman da ke binciken satar Mai da lalacewar kayan samar da shi a yankin Neja Delta.
Sanata mai wakiltar Delta ta Arewa, Ned Nwoko, wanda shi ne shugaban kwamitin, ne ya gabatar da rahoton a zauren majalisar a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa binciken ya gano asarar kuɗaɗe sama da Dala Biliyan 300 daga ribar Man da ba a bayyana ba tsawon shekaru.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa rahoton ya ba da shawarar aiwatar da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa na auna Mai a duk wuraren hakowa da tashoshin fitar da shi, tare da bukatar hukumar kula da harkokin man fetur ta sama (NUPRC) ta samar da na’urorin zamani na aunawa ko kuma a mayar da wannan aiki ga sashen nauyi da aunawa na ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da saka jari ta tarayya.
Rahoton ya kuma bukaci gwamnatin tarayya ta samar da kayan aikin sa ido na zamani kamar jiragen sama marasa matuki don taimakawa jami’an tsaro wajen yaki da satar mai.
Haka kuma an ba da shawarar kafa Asusun Kula da Harkokin Teku domin inganta horo, tsaro, da kiyaye lafiyar harkokin jiragen ruwa.
Kwamitin ya kuma bukaci a kafa kotu ta musamman domin gurfanar da masu satar Mai da abokan harkokinsu cikin gaggawa, tare da aiwatar da tsarin asusun raya al’ummomin masu dakoknan da dokar masana’antar Mai (PIA) ta tanada, domin rage lalata kayayyaki da satar Mai.
Rahoton ya ƙara da cewa duk rijiyoyin da aka daina amfani da su ko aka rufe su gaba ɗaya a mika su ga hukumar NUPRC wacce za ta miƙa su ga ƙananan matatun Mai don rage satar mai da kuma ƙara samar da Man da ake amfani da shi a cikin gida.
Kwamitin ya nemi izini daga majalisar dattawa domin bibiyar asusun kuɗaɗen da aka sata cikin gida da ƙasashen waje, inda rahoton kwararru ya nuna cewa akwai fiye da Dala Biliyan 22, biliyan 81, da biliyan 200 da ba a bayyana asalin su ba a lokuta daban-daban.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yaba wa kwamitin bisa irin aikin da ya yi, inda ya ce majalisar za ta tattauna batutuwan da ke cikin rahoton bayan an kammala cikakken rahoto na ƙarshe.
Ya kuma umurci kwamitin da ya ci gaba da bincike har sai an samar da rahoton ƙarshe mai cike da cikakkun bayanai.













































