ASUU ta musanta ikirarin gwamnatin Tarayya na biyan bashin Naira Biliyan 50

ASUU ASUU NEW

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta bayyana cewa ba ta karɓi kuɗin farfaɗo da jami’o’i na Naira biliyan 50 da gwamnatin tarayya ta ce ta saki ba, tana mai cewa babu ɗaya daga cikin bukatun da ta gabatar da aka biya kafin babban taron kwamitinta na ƙasa da za a gudanar a ranar 8 da 9 ga watan Nuwamba, 2025.

ASUU ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Farfesa Jurbe Molwus ya fitar a ranar Laraba, inda ya tuna cewa kungiyar ta dakatar da yajin aikin gargadi na mako biyu cikin amincewa, bayan alkawuran da jami’an gwamnati suka yi cewa za a kawo sabbin shawarwari da za su warware matsalolin da ake fama da su.

Kungiyar ta ce yayin da take shirin gudanar da babban taronta, ta yi tsammanin gwamnati za ta biya wasu daga cikin haƙƙoƙin da ake bin malaman jami’o’i kamar albashin watanni uku da rabi da aka dakatar, bashin karin albashi na kashi 25 da 35 cikin ɗari, bashin karin girma da sauran albashin da ba a biya ba, amma abin da ke fitowa daga gwamnati kawai shi ne sanarwar ministan ilimi, ba biyan kuɗi ba.

ASUU ta ce ikirarin gwamnatin tarayya na sakin Naira biliyan 50 bai kai jami’o’i ba, tana tambayar dalilin da ya sa ministan ilimi Dakta Tunji Maruf Alausa ke riƙe da kuɗin.

Haka kuma ta musanta ikirarin ministan na cewa Naira biliyan 2.3 aka saki domin biyan bashin albashi da karin girma, tana mai cewa babu wani malami da ya karɓi irin wannan kuɗi.

Kungiyar ta bayyana cewa adadin Naira biliyan 2.3 da gwamnati ta ambata ba zai iya biya bashin albashi da karin girma na dukkan jami’o’in tarayya ba, har ma ta kira wannan adadi a matsayin abun raina hankali saboda ƙarancinsa, domin a cewarta bai wuce ya biya manyan jami’o’i uku kacal ba.

ASUU ta bukaci ‘yan Najeriya, ɗalibai da iyaye su riƙa dora alhakin matsalar ga gwamnatin tarayya, tana gargadin cewa za ta koma yajin aiki idan har ba a biya bukatunta ba kafin ranar 21 ga watan Nuwamba, 2025, lokacin da wa’adin makonni huɗu da ta baiwa gwamnati zai ƙare.

Kungiyar ta jaddada cewa dakatar da yajin aikin da ta yi ya kasance ne don nuna kyakkyawar niyya a tattaunawar da take da gwamnati, don haka ta bukaci a biya haƙƙokin malaman cikin gaggawa domin kauce wa sake komawa yajin aiki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here