Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Kungiyar kwadago ta sake yin watsi da sabon kudirin biyan mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya ta yi.
Kungiyar Kwadago da ta kunshi kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kuma TUC a ranar Talata ta yi watsi da tayin gwamnatin tarayya na biyan Naira Dubu 60,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi.
Kungiyar Kwadago ta kuma sauya filaye daga matsayinta na Naira Dubu 497,000 a makon jiya zuwa Naira Dubu 494,000.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa ta kira Sanata Abdul Ningi bayan dakatar da shi
Wani fitaccen mamba a kwamitin na tattaunawa kan batun karin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya ya shaidawa wakilin kungiyar kwadago ta Channels cewa gwamnatin tarayya da kungiyoyin masu zaman kansu sun gabatar da shawarar biyan Naira Dubu 60,000 a duk wata sabanin Naira Dubu 57,000 da suka gabatar makon da ya gabata lokacin da kwamitin ya hadu a karshe.
Tun da farko dai gwamnati ta gabatar da kudi naira Naira Dubu 48,000 da kuma Naira Dubu 54,000 a makon da ya gabata, wadanda kuma kungiyar kwadago ta ki amincewa da su.