Yilwatda ya ziyarci Gwamnan Kano, ya jaddada tsarin rabon shugabanci 60/40

APC Nentawe Yilwatda new

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai ziyarar girmamawa ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya bayyana gamsuwarsa da yawan magoya baya da shugabannin jam’iyya da suka halarci taron.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Litinin.

Farfesa Yilwatda ya sake jaddada tsarin rabon shugabancin jam’iyya na 60/40 tsakanin sabbin mambobin da suka sauya sheka da tsoffin mambobin APC, yana mai cewa tsarin an tsara shi domin inganta haɗa kai, ƙarfafa zumunci da tabbatar da cikakken sa hannu na dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin jam’iyya da mulki.

Ya ce ya yi matuƙar jin daɗin yadda jama’a suka amsa kiran taron, yana mai cewa yawan mahalarta ya nuna cikakken haɗin kai, ƙwazo da jajircewa a tsakanin mambobin APC a Jihar Kano.

A cewarsa, wannan taro mai ƙarfi wata alama ce mai kyau da za ta ƙara ƙarfafa goyon baya ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu tare da ƙarfafa damar sa a manyan zaɓuka masu zuwa.

Farfesa Yilwatda ya yaba wa Alhaji Yusuf Gawuna da Sanata Barau Jibrin bisa jingine burinsu na kashin kai da kuma mara wa hangen nesan gwamnan baya domin cigaban jam’iyya a Kano.

Haka kuma ya yabawa Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan jagoranci da gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa jam’iyya da tabbatar da haɗin kai a jihar.

A nasa jawabin, Gwamna Yusuf ya gode wa shugabannin APC kan ziyarar da suka kai da kuma ci gaba da goyon bayan haɗin kai da zaman lafiya a Kano.

Ya sake jaddada kudurinsa na yin aiki tare da jam’iyya da mambobinta domin tabbatar da cewa jihar ta kasance dunkulalliya, mai wadata, kuma mai tafiya da Ajandar Sabuwar Fata ta ƙasa.

Gwamna Yusuf ya ce yawan mahalarta taron da goyon bayan da aka nuna sun tabbatar da cewa mambobin APC a Kano a shirye suke su yi aiki tare domin alherin jam’iyya da al’ummar jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here