Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin ta bayar da Naira Biliyan 5 a matsayin tallafin gaggawa ga ‘yan kasuwar da gobara ta shafa a babbar Kasuwar Singer da ke Kano.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya sanar da bayar da tallafin yayin da ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya domin jajantawa ‘yan kasuwar a madadin Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu.
Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa gwamnonin APC karkashin kungiyar Gwamnonin Jam’iyya Mai Ci (PGF) su ma sun bayar da Naira Viliyan 3 ga wadanda gobarar ta shafa.
Shettima ya jajanta wa ‘yan kasuwar tare da yin addu’ar Allah ya hana sake aukuwar gobara a kasuwar.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma karɓi Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da magoya bayansa zuwa jam’iyyar APC a madadin Shugaban Ƙasa.
Shettima ya sake jaddada tabbacin da Tinubu ya bayar cewa matsayin gwamnan a cikin jam’iyyar ba shi da tamka.
Ya ce matakin gwamnan na shiga jam’iyya mai mulki ya ƙarfafa ƙudurin gwamnatin Tinubu da jam’iyyar wajen gina ƙasa mai haɗa kowa da kowa da wadata.
Shettima ya bayyana Kano a matsayin jiha mai karɓar kowa da kowa, wadda ke rungumar bambance-bambance ta mai da su dama.
Ya ce gudunmawar Kano ga Najeriya ta wuce lissafin zaɓe kaɗai.
Ya tuna cewa Kano ta bai wa Najeriya manyan jagorori da suka sauya tafarkin siyasa da tunanin ƙasa, ciki har da marigayi Maitama Sule da Aminu Kano.
Shettima ya bayyana Gwamna Yusuf a matsayin ɗan Kano mai hangen nesa, yana mai cewa tafiyarsa ta siyasa na nuni da makomar Najeriya.
Ya jajanta wa gwamnan kan gobarar da ta auku a Kasuwar Singer, tare da tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta yi aiki tare da jihar domin tallafa wa duk waɗanda abin ya shafa.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya ce komawar gwamnan APC na nufin Kano ta koma tsakiyar siyasar Najeriya kuma za ta amfana da gwamnatin tarayya.
Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce shigowar Yusuf APC abu ne mai muhimmanci ga jam’iyyar, yana mai cewa makomar Kano za ta fi haske.
Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya ce gwamnan ya ɗauki mataki mai kyau ta shiga APC, yana mai cewa jihar za ta ci moriyar hakan.
Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyya APC Hope Uzodimma, ya ce Yusuf ɗan asalin APC ne wanda ya fita na ɗan lokaci kuma ya dawo gida.
A nasa jawabin, Gwamna Yusuf ya ce shiga APC wata muhimmiyar rana ce ga jihar, yana mai cewa manufar siyasa ita ce yi wa jama’a hidima.
Ya ce ya shiga APC ne domin samar da sakamako mai amfani ga al’ummar Kano, yana mai cewa duk matakan da ya ɗauka a matsayin gwamna sun kasance ne domin inganta rayuwar jama’a.













































