‘Yan Sanda Sun Kama Masu Safarar Mutane Da Yara 59

Suspected trafficked children 750x430

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya (FCT) ta ce jami’anta sun kama wasu da ake zargi da safarar mutane tare da yara 59.

Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Tunji Disu, ya ce tawagar karkashin jagorancin Sarki Umar, mataimakin Sufeton ‘yan sanda (DSP), sun tare wata farar motar bas mai dauke da kujeru 15 na Peugeot, wadda aka fi sani da J5, a ranar 6 ga watan Janairu yayin da take kan hanyar zuwa jihar Nasarawa.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce motar bas din tana daukar yaran ‘yan tsakanin shekaru hudu zuwa 12 ne, wadanda ake zargin ana safarar su ne daga Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here