Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya ta fara matakin ƙarshe na tattaunawa da ƙungiyar malaman jami’o’i ASUU

Alausa minister 750x430 (1)

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta fara matakin ƙarshe na tattaunawa da ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU da sauran ƙungiyoyin ma’aikatan manyan makarantu.

Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a birnin Abuja a ranar Laraba yayin taron ƙungiyar masu aikin fasaha da ke duba yanayin aikin malamai na jami’o’i.

Ya bayyana cewa akwai kyakkyawan fata cewa za a kammala duk batutuwan da ke saura domin kaucewa sake samun yajin aiki a manyan makarantu.

Ya ce ƙungiyar ta na kammala shirin amsar da za ta mika wa ƙungiyoyin ta hanyar kwamiti mai kula da tattaunawa da ƙungiyoyin jami’o’in gwamnatin tarayya.

Wannan, in ji shi, wani mataki ne na bin umarnin shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu na cewa a tabbatar ɗalibai ba sa rasa karatu saboda yajin aiki.

Alausa ya ce kwamitin da aka kafa a farkon makon nan ya shiga zurfin tattaunawa domin hanzarta cimma yarjejeniya da aiwatar da shawarwarin da aka cimma.

Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta riga ta biya Naira biliyan 50 na ƙarin kuɗin aiki na malamai.

Labari mai alaƙa: Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da kwamitin tattaunawa domin shawo kan barazanar yajin aikin ASUU da NASU

Haka kuma, ya ƙara da cewa an ware Naira biliyan 150 a kasafin kuɗin 2025 domin nazarin bukatun jami’o’i, kuma za a raba su gida uku inda kaso na farko biliyan 50 za a kashe nan kusa.

Ya kuma ce, gwamnati tana da niyyar ganin malamai da ma’aikata sun samu abin da ya dace da su, kodayake ba za a iya ba su komai lokaci guda ba.

Ministan ya bayyana cewa an riga an warware batutuwan da suka shafi bashin karin matsayi da sauran alawus-alawus, yayin da sauran kuɗaɗen da suka rage za a biya su kafin ƙarshen shekara ta 2026.

Sannan ya yi kira ga ƙungiyoyin malamai da ma’aikata su ci gaba da nuna haƙuri yayin da gwamnati ke aiki wajen kammala komai cikin gaskiya da amana.

A ƙarshe, Alausa ya bayyana cewa, a karon farko, lauya na tarayya da jami’an ma’aikatar shari’a suna cikin tattaunawar kai tsaye domin tabbatar da cewa duk yarjejeniyar da aka cimma tana da ingantaccen tushe na doka kuma za ta iya zama abin bin doka.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here