Gwamnatin jihar Kwara ta ayyana Litinin a matsayin ranar hutu ga malamai

AbdulRahman AbdulRazaq

Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ranar Litinin, 6 ga Oktoba, 2025, a matsayin ranar hutu ga malamai domin bikin Ranar Malamai ta Duniya.

Kwamishinan Ilimi da cigaban ɗan Adam, Dakta Lawal Olohungbebe, ne ya isar da sakon gwamnan inda ya yaba wa jajircewar malamai, da kuma sadaukarwarsu wajen ci gaban al’umma.

Ya bayyana malamai a matsayin muhimman ginshiƙai wajen ci gaban ɗan Adam da haɓaka ƙasa, yana mai cewa suna taka rawar gani wajen gina makomar al’umma.

Wannan sanarwa ta fito ne daga Ilorin a ranar Asabar, inda gwamnatin jihar ta bayyana cewa bikin na bana zai kasance lokaci na tunawa da muhimmancin malamai a tsarin rayuwar ɗan Adam.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here