A ranar Alhamis 7 ga watan Maris ne ‘ƴan fashin daji suka shiga wata makarantar gwamnati a garin Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna, suka sace ɗalibai zama da mata fiye da 280.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ɗaliban suka kammala taron safe, inda ‘ƴan bindigar suka yi wa makarantar ƙawanya tare da kora ɗaliban zuwa cikin daji.
Karin labari: ‘Ƴan sanda sun kama jami’in da ya harbi wani mutum a kasuwar Wuse
Ɗalibin wanda ya kuɓuta ya bayyana cewa ya kwanta ne a cikin ciyawa, inda ya riƙa jan ciki kafin ya samu wurin buya.
A karshe ɗalibin ya bayyana irin wahalar da ya sha kafin samun kuɓuta da kuma halin da sauran ɗalibai suka kasance a ciki.
Sannan ya bayyana yadda ya samu komawa cikin gari bayan yin tafiya mai tsawo a cikin daji.