Dakataccen Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, ya halarci bikin binne gawa tare da ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike, a Fatakwal.
Sa’o’i kaɗan da suka gabata, Fubara da Wike sun halarci taron zaman lafiya da aka yi da daddare wanda shugaba Bola Tinubu ya shirya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A ranar Asabar ne mai magana da yawun Ministan, Lere Olayinka, ya wallafa wani saƙo a shafin X wanda ya ke bayyana cewa, Wike ya kasance a Fatakwal don binne kawunsa.
“Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, tare da dakataccen gwamna Siminalayi Fubara, da shugaban majalisar dokokin jihar Rivers Martins Amaewhule sun haɗu a wajen jana’izar kawun Wike a Rumuepirikom da ke jihar Rivers a yau,” kamar yadda Olayinka ya wallafa.

Wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas, da Martin Amaewhule, dakataccen shugaban majalisar su ma sun halarci zaman sulhun na ranar Alhamis.
Wike da Fubara sun fara rikici ne game da bambance-bambancen siyasa tun a shekarar 2023.
Rikicin nasu ya kai ga rushewar majalisar dokokin jihar Rivers.
A ranar 18 ga Maris ɗin bana ne shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Rivers saboda rikicin siyasa da kuma hare-haren da ake kaiwa gidajen man fetur a jihar.
Shugaban ya kuma dakatar da Fubara da ’yan majalisar Rivers tare da naɗa wanda zai kula da al’amuran jihar na tsawon watanni shida.













































