Tsohon babban Sakataren hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da murkushe ‘yan adawa tare da toshe masu suka.
Da yake magana a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a ranar Lahadi, Yusuf ya yi zargin cewa tsare shi da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati (EFCC) ta yi a baya-bayan nan na daga cikin yunkurin rufe shi da gangan. “Wannan gwamnati ta hana ni beli da gangan don ta jikkata ni… duk don ta yi kokarin kashe ni. Amma ni ba mutumin da zai yi shiru ba ne,” in ji shi.
A watan Fabrairu ne dai hukumar EFCC ta gurfanar da Yusuf a gaban babbar kotun tarayya bisa zarginsa da laifin zamba, sai dai ya musanta aikata laifin.
Da yake bayyana al’amuran da suka kai ga tsare shi, Yusuf ya ce jami’an EFCC sun kai farmaki gidansa a ranar 29 ga watan Janairu ba tare da gabatar da sammacin kama shi ba. “Sun shiga gidan suka ce suna son ganina, wai ina jiransu, sai daga baya suka nuna bajojin su,” in ji shi.
Ya bayyana yadda jami’an ‘yan sandan suka hana shi canza kaya tare da hana matarsa ba ta ba shi kaya, sannan yayin da suke tafiya jami’an suka yi masa kamu “kamar sun kama wani fitaccen mai laifi kamar Kachalla ko Bello Turji,”.
Karin karatu: Ba zan shiga haɗakar Atiku ba – Gwamna Buni
Yusuf dai ya shafe kwanaki shida a hannun EFCC kafin a gurfanar da shi a gaban kuliya, daga bisani kuma aka ki bayar da belinsa, matakin da ya ce ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa. “Beli wani hakki ne da tsarin mulki ya amince da shi ga duk wanda ake tuhuma, sai dai a cikin laifukan kisa ko ta’addanci, kuma shari’a ta ba ta kasance ba irin wannan ba,” in ji shi.
Kin amincewa da belin ya tilasta wa Yusuf karin kwanaki 24 a gidan yarin Kuje.
“Sukar gwamnati a tsarin dimokuradiyya hakki ne na kowane dan kasa, amma yanzu shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana kokarin murkushe ‘yan adawa da mayar da Najeriya kasa mai mulkin kama karya na jam’iyya daya, ba za mu bari hakan ta faru ba.”
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Yusuf a matsayin babban sakataren hukumar NHIS a shekarar 2016. Ministan lafiya da hukumar NHIS sun dakatar da shi a shekarar 2017 da kuma 2018 bisa zargin cin hanci da rashawa, kuma daga karshe an cire shi daga mukaminsa a shekarar 2019.













































