Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sen. Iyorchia Ayu, zai fara ziyarar kwanaki 14 a nahiyar to farawa daga ranar laraba.
Mai baiwa shugaban jam’iyyar PDP shawara na musamman kan harkokin labarai, Simon Imobo-Tswam ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.
Imobo-Tswam wanda bai bayyana hakikanin dalilin tafiyar Ayu zuwa turai ba, ya ce ana sa ran shugaban zai dawo Najeriya nan da karshen watan Satumba.
“Yayin da ya tafi, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar mai kulada shiyyar Amb. Iliya Damagun zai maye gurbin aikin Ayu.
“Tuni shugaban dai ya mikawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC bayanai na mika mulki,” in ji shi.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya rawaito cewa majalisar zartaswar jam’iyyar ta kasa ta kada kuri’ar amincewa da Ayu a ranar 8 ga watan Satumba.
Idan za a iya tunawa akwai kiraye-kirayen da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka yi cewa ya kamata Ayu ya sauka daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar PDP.
Rahotanni sun ce jimillar mambobi 397 da suka hada da shuwagabannin jam’iyyar na kasa, tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da sauran su ne aka amince da taron.
Dukkan ‘yan majalisar gudanarwar jamiyar su 397 da suka halarci taron sun kada kuri’ar goyon bayan Ayu ya ci gaba da zama shugaban jam’iyyar.
Mukaddashin shugaban kwamitin amintattu kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Adolphus Wabara ne ya kada kuri’ar bayan da shugaban marasa rinjaye na majalisar ya gabatar da bukatar mambobin kwamitin su ci gaba da rike shi a matsayin shugaban jam’iyar.













































