Jana’izar da za a yi wa Sarauniya Elizabeth II ranar Litinin za ta kasance daya daga cikin manyan taruka da aka hada sarakuna da ‘yan siyasa a Birtaniya a cikin shekaru aru-aru.
A karshen makon jiya ne aka aka da takardun gayyatar zuwa jana’izar ga shugabanni da sarakuna da sauran manyan mutane a fadin duniya, inda ake sa ran shugabannin kasashe da manyan mutane fiye da 500 za su halarce ta.
An shaida wa galibin shugabannin cewa su halarci jana’izar a jiragen sama na ‘yan kasuwa inda kuma aka gaya musu cewa za a dauke su a motocin bas daga filin jiragen saman zuwa yammacin London.
Za a yi taron jana’izar ne a babban dakin Westminster Abbey, wanda zai iya daukar kusan mutum 2,200.
Ga abubuwan da muka sani game da mutanen da za su halarci jana’izar da wadanda ba za su je ba.
Sarakunan kasashen Turai, wadanda da dama daga cikinsu suna da alaka ta jini da Sarauniyar Ingila, na cikin wadanda ake sa ran za su halarci jana’izarta.
Sarkin Belgium Philippe da Sarauniya Mathilde sun tabbatar da cewa za su halarci jana’izar, yayin da shi ma Sarki Willem-Alexander da matarsa, Sarauniya Maxima, tare da mahaifiyarsa, tsohuwar sarauniyar Dutch Gimbiya Beatrix za su halarci jana’izar.













































