Rahotanni daga Abuja sun bayyana cewa ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya yi ganawar sirri da takwaransa na NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa an yi ganawar ne a gidan Kwankwason a Abuja a yammacin yau Talata.
Wata majiya da ke kusa da Kwankwaso ta ce ta na tunanin shugabannin biyu sun tattauna ne a kan shari’ar Atiku da Tinubu a Tirabunal da kuma yanayin kunci da ake fama da shi a kasar sakamakon cire tallafin mai.
Sai dai kuma babu tabbacin ko Atiku din ya zo neman sulhu ne ga Kwankwaso bayan sun samu saɓani gabanin zaben shugaban kasa na 2023, lamarin da ya sanya tsohon gwamnan ya fice da ga PDP ya koma NNPP.













































