Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya sanya hannu kan wata dokar da ya ayyana a yammacin Larabar makon nan ta haramta wa ‘yan kasashen duniya 12 shiga Amurka.
Kasashen da abin ya shafa sun hada da Afghanistan da Myanmar da Chadi da Congo, sai Equatorial Guinea da Eritrea da Haiti da Iran, sai Libya da Somalia da Sudan da kuma Yemen.
Dukkan yan waɗannan ƙasashe za a hana su izinin shiga Amurka bisa ga sanarwar da shugaban ya sanya wa hannu.
Haka kuma, za a takaita shigowar ‘yan kasashen Burundi da Cuba da tsiburin Laos, sai Saliyo da Togo da Turkmenistan da kuma Venezuela.
Trump ya ce ana bukatar daukar matakin ne domin kare Amurka daga kwararar yan ta’adda na kasashen waje da kuma kare ta daga barazanar tsaro.
“Ba za mu ƙyale mutanen da ke son yi mana lahani su shigo mana cikin ƙasarmu ba,” in ji Trump ta cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin X.
Ya ce kasashen da ke da tsauraran takunkumi sun kuduri aniyar magance yawan kasancewar ‘yan ta’adda ne a cikinsu”.
Ya yi zargin cewa wasu sun kasa ba da hadin kai kan tsaro ta hanyar biza kuma suna da gazawa wajen tabbatar da asalin matafiya, rashin isassun bayanan tarihin laifuka da kuma yawan adadin biza a Amurka.













































