Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya NRC, ta nemi afuwar fasinjoji bisa jinkirin da aka samu na rashin jigin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Manajan Tashar Jiragen kasa ta Abuja zuwa Kaduna (AKTS), Pascal Nnorli, ya ce an samu tsaikon ne sakamakon karancin man dizal.
Kamfanin na layin dogo ya kara da cewa an samu tsaikon ne sakamakon “samar da man dizal da AGO, wanda ya gaza cika ka’idojin da ake bukata don sarrafa kayayyakin mu, wanda aka ki amincewa da shi bayan gwajin dakin gwaje-gwaje kamar yadda doka ta tanada.”












































