Kungiyar kare hakkin musulmi MURIC ta caccaki kungiyar kiristoci ta ƙasa CAN bisa kin amincewa da matakin da jihohin Bauchi, Katsina, Kano, da Kebbi suka dauka na rufe makarantu a watan Ramadan.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 3 ga Maris 2025, Babban Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya zargi CAN da yin katsalandan a cikin al’amuran Musulmi da kuma yunkurin haifar da ruɗani a lokacin da suke kokarin magance matsalolin addini.
A baya dai kungiyar CAN ta yi Allah-wadai da rufe makarantun, inda ta ce matakin na nuna wariya ga daliban Kirista da kuma kawo cikas ga harkokin ilimi.
Har ma shugaban kungiyar CAN, Archbishop Daniel Okoh, ya yi gargadin cewa kungiyar na iya daukar matakin shari’a idan ba a sauya manufar ba, yana mai jaddada cewa ilimi wani hakki ne na asali don haka bai kamata a yi kasa a gwiwa ba saboda dalilai na addini.
Labari mai alaƙa: Kungiyar kiristoci ta yi barazanar maka jihohi Arewa 4 sakamakon rufe makarantu saboda watan Ramadan
Sai dai MURIC ta yi watsi da damuwar kungiyar ta CAN, inda ta bayyana cewa azumin watan Ramadan na musulmi ne, kuma mafi yawan al’ummar musulmi a jihohin da abin ya shafa na da ‘yancin yanke shawara domin amfanin su.
MURIC ta kara da cewa dimokuradiyya tana goyon bayan muradin mafi rinjaye kuma gwamnatocin jihohin da abin ya shafa suna yin aiki ne kawai da abin da al’ummar musulmi suke so.
Kungiyar ta kuma zargi kungiyar ta CAN da munafunci, inda ta ce duk da cewa ta yi tofin Allah tsine kan manufofinta a jihohin da musulmi ke da rinjaye, ta yi watsi da halin da musulmin ke ciki a wasu yankuna.
Kungiyar MURIC ta bukaci kungiyar ta CAN da ta mutunta ayyukan addinin Musulunci tare da daina tsoma baki a harkokin addinin Musulunci.