Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya kaddamar da wani kwamitin bincike na musamman mai mutum takwas (SIP) domin gudanar da bincike kan rikicin da ya barke a yayin jerin gwanon tawagar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, bayan Sallar idi a ranar Lahadi 30 ga Maris, 2025.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Laraba, ya ce an dorawa kwamitin alhakin gano musabbabin tashin hankalin tare da tantance ko an bijirewa dokar da rundunar ta haramta na hana duk wani nau’in hawa ko hawan doki a duk lokacin bukukuwan Sallah.
SolaceBase ta ruwaito cewa rundunar ‘yan sanda ta haramta duk wata harkar hawan sallah a ranar Juma’ar da ta gabata saboda matsalar tsaro a jihar.
Sai dai kuma a ranar Idi, an ruwaito wani lamari da ya yi sanadin mutuwar wani dan banga mai suna Surajo Rabi’u dan unguwar Sabo Titi Jaba, yayin da wani mai suna Aminu Suleman daga Kofar Mata ya samu raunuka kuma a halin yanzu yana jinya a asibitin Murtala Mohammad da ke Kano.
Hakazalika, an kama wasu mutane biyu wadanda aka bayyana sunayensu, Usman Sagiru mai shekaru 20 da haihuwa dan unguwar Sharifai da Nasir Idris mai shekaru 35 a Kofar Mazugal, da laifin faruwar lamarin.
Kazalika, rundunar ‘yan sandan ta gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, domin amsa tambayoyi kan zargin bijirewa dokar hana hawan sallah.
An umurci kwamitin bincike na musamman da ya gaggauta bincikensa domin tabbatar da an yi adalci. “Duk wanda aka samu da laifi za a sanya shi ya fuskanci fushin doka,” in ji sanarwar.
Rundunar ‘yan sandan ta sake jaddada haramta duk wani nau’in ayyukan daba tare da gargadin cewa duk wanda aka samu yana aikata irin wadannan ayyukan za a hukunta shi da gaske.