Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa rundunar aiki ta musamman nan take domin tinkarar barazanar tsaro a tashoshin mota da sauran muhimman wuraren taruwar jama’a a faɗin jihar Kano.
Wannan mataki na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda ta bayyana cewa an ɗauki wannan shawara ne domin hana shigar masu aikata laifuka da kuma kare lafiyar jihar Kano baki ɗaya.
Sanarwar ta nuna cewa gwamnan ya ƙuduri aniyar ƙarfafa tsaro musamman a manyan hanyoyin shiga da fita na birnin Kano, ganin yadda tashoshin mota ke da yawan zirga-zirgar mutane da kuma tasirin abubuwan tsaro na baya-bayan nan da suka faru a wasu wurare.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an gano tashoshin mota a matsayin wurare masu haɗari saboda yawaitar motsin mutane, tare da wasu abubuwan tsaro da suka faru kwanan nan, ciki har da kama wasu da ake zargi da aikata laifuka a tashar mota ta Kofar Ruwa.
Karin labari: Gwamnatin Kano ta haramta ƙungiyar Hisbah mai zaman kanta, ta bayar da umarnin kama mambobinta
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa rundunar aikin za ta gudanar da tsauraran ayyukan sa ido, tattara bayanan sirri, da haɗin gwiwar ayyukan tsaro a tashoshin mota da sauran wuraren da ake ganin suna da rauni, tare da faɗaɗa ayyukan zuwa wurare kamar gidajen mai da sauran wuraren jama’a da mutane ke yawan taruwa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa wannan mataki na matsayin rigakafi ne domin dakile barazana tun kafin ta ƙara girma, da ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, da kuma dawo da amincewar al’umma.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba ta yarda da aikata laifuka ba kuma za ta ci gaba da ba wa hukumomin tsaro cikakken goyon baya wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.












































