“NLC ba ta tuntuɓe mu kafin ayyana yin zanga-zanga a fadin Najeriya ba” – TUC

NLC, TUC, zanga-zanga, najeriya
Kungiyar Kwadago ta TUC ta yi ikirarin cewa kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ba ta tuntube ta kafin ta kuduri aniyar gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu a...

Kungiyar Kwadago ta TUC ta yi ikirarin cewa kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ba ta tuntube ta kafin ta kuduri aniyar gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu a fadin kasar a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairun 2024 ba.

Babban sakataren kungiyar Nuhu Toro a wata wasiƙa da ya aike wa shugabannin NLC ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda kungiyar kwadago karkashin jagorancin Joe Ajaero ba ta tuntuɓi ƙungiyar ‘yan kasuwa da Festus Osifo ke jagoranta ba kafin ta dauki matakin.

Karin labari: An rage ranakun aikin gwamnati zuwa kwana 3 a Legas

Kungiyoyin biyu dai sun baiwa gwamnati wa’adin kwanaki 14 da ta aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla kan magance matsalar tattalin arziki da ke kara ta’azzara ƙasar, ko su tafi yajin aiki.

Tuni dai hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta buƙaci kungiyar ƙwadago ta NLC ta jingine yajin aikin da ta shirya yi ta kuma shiga tattaunawa a maimakon daukar matakan da za su iya tayar da zaune-tsaye, amma ƙungiyar da Ajaero ke jagoranta ta dage kan ci gaba da matakin da ta ɗauka na zuwa yajin aiki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here