Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da cewa ma’aikatan gwamnati daga mataki na 1 har zuwa na 14 za su fara zuwa aiki kwana uku a mako a wani mataki na saukaka kalubalen tattalin arzikin da mazauna jihar ke fuskanta.
Ya yi magana ne a wata hira ta kai tsaye a kafar yaɗa labarain ‘Sanwo Speaks’ domin jan hankalin mazauna yankin kan matakan da ake dauka na rage nauyin raɗadin tattalin arzikin da ke kan ‘yan Legas.
Karin labari: Sojin Mozambik sun daƙile yunƙurin ɗaukar ma’aikata tsageru
To sai dai matakin bai shafi malaman makaranta ba, inda ya ce su za su ci gaba da zuwa aiki na tsawon kwana biyar a mako.
Gwamnan Sanwo-Olu ya ce gwamnati za ta yi duk abin da ya kamata domin ƙarawa malaman makarantar tallafin sufuri.