Majalisar tattalin arzikin ƙasa NEC ta amince da ware Naira Biliyan 100 domin gyaran cibiyoyin horas da jami’an tsaro a faɗin Najeriya, wanda za a fara aiki bayan sahalewar shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Amincewar ta biyo bayan rahoton kwamitin da aka kafa domin tantance halin da cibiyoyin horas da jami’an tsaro ke ciki, inda kwamitin ya gano cewa yawancin su sun lalace kuma suna buƙatar gyara cikin gaggawa.
A zaman majalisar na 154 da aka gudanar ta internet ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ta kuma amince da Naira Biliyan 2.6 domin aikin ba da shawara kan aiwatar da wannan shiri.
Tun a watan Oktoba a zama na 152, shugaban ƙasa ya bayar da shawarar sake fasalin makarantun horaswa domin tabbatar da ingantaccen horaswa ga jami’an tsaro a matakai daban-daban a faɗin ƙasa.
Gwamanan jihar Enugu, Peter Mbah, wanda ya jagoranci kwamitin, ya bayyana wa majalisar cewa matsalar ta lalacewar gine-gine da kayan aiki na bukatar kulawa cikin gaggawa saboda yadda take ƙara shafar ingancin horaswa.
Karanta: Majalisar Dattawa ta tabbatar da tsohon babban Hafsan tsaron Najeriya a matsayin ministan tsaro
Bayan gabatarwar, mataimakin shugaban ƙasa Shettima ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da daukar matakai domin magance matsalar tare da yin kira ga gwamnonin jihohi su tabbatar da cewa sauye-sauyen tattalin arziki da ake aiwatarwa suna amfani kai tsaye ga al’umma.
Ya jaddada cewa duk gwamnatocin da ke da alhakin gudanar da mulki su mayar da hankali kan aikace-aikace maimakon magana kawai, don tabbatar da cewa sakamakon ayyuka ya bayyana ga jama’a a fannonin kasuwanni, makarantu da cibiyoyin lafiya da gonaki.
Ya bayyana cewa manufar gwamnati ita ce samar da sauyi mai gamsarwa da jama’a za su iya gani da ji a rayuwarsu ta yau da kullum, tare da mayar da hankali kan ingantaccen aiwatarwa a dukkan matakai.













































