Mutumin da ya kutsa gaban Tinubu a Kaduna ya na da taɓin hankali- Ƴan sanda

Bola Ahmed Tinubu new 640x430

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta ce, mutumin da ya yi yunkurin karya tsarin tsaro a ziyarar da Shugaba Bola Tinubu ya kai jihar inda ya kutsa wajen shugaban ba shi da hankali.

Tinubu ya je Kaduna ne domin ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Uba Sani, ta aiwatar kuma ya na gabatar da jawabi ne wani mutum da ‘yan sanda suka bayyana sunansa Umar Muhammed ya katse jawabin shugaban kasar a lokacin da ya yi kokarin tunkarar shi.

Sai dai nan da nan dogarin tsaro na Tinubu ya hana shi, amma shugaban ya buƙaci a bar shi ya ƙarasa idan ba ya ɗauke da abun cutarwa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴan sanda Kaduna Mansir Hassan ya fitar, ya ce bincike ya nuna cewa an haifi Umar Mohammed da lalurar taɓin hankali”.

Hassan ya ce, da aka yi masa tambayoyi, Umar Mohammed, ya bayyana cewa ya dade yana sha’awar ganawa da shugaban ƙasa da gwamna kuma ya yi hakan ne saboda jin daɗin kansa.

Faifan bidiyon da ke nuna wani matashin mai goyon jam’iyyar APC da ya yi yunkurin tunkarar wani yanki da aka killace yayin wani taron da aka yi kwanan nan a dandalin Murtala Square da ke Kaduna,” in ji sanarwar.

“Mutumin da ake magana a kai shi ne Umar Mohammed, haifaffen Anguwan Muazu a Kaduna, an haife shi da taɓin hankali.

“Shi mutum ne mai tsananin goyon bayan Shugaban kasa da Gwamna kamar yadda bincikenmu ya nuna, amma duk da haka an tantance shi aka shigar da shi filin a matsayin mai goyon bayan jam’iyyar APC, sanye da rigar yakin neman zabe, dauke da tutoci masu dauke da hotunan Shugaban kasa da Gwamna, kamar yadda duk wani mai goyon bayan da aka tantance aka shigar da shi filin wasan da tawagar tantancewar ta gudanar.

A nasa ɓangaren kwamishinan ƴan sandan jihar Kaduna Rabi’u Muhammad, ya ja kunnen waɗanda ke yaɗa faifan bidiyo domin yaudarar mutane da su daina ko kuma su kuka da kansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here