Mutum 80 sun mutu a turmutsutsun rabon kayan sallah a Yemen

4cb28087 8dc5 4627 893c da23bf958e86
4cb28087 8dc5 4627 893c da23bf958e86

Mayakan ƙungiyar Houthi sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 80 a wani turmutsutsu da ya auku yayin rabon kayan ƙaramar sallah a Sanaa babban birnin Yemen.

Ɗaruruwan mutane ne ciki har da ƙananan yara suka taru a wata makaranta domin karɓar tallafin kayan sallah.

Jami’an kungiyar Houthi da ke da iko da birnin sun ce lamarin ya auku ne a yankin Bab-al-Yemen.

Wakilin BBC ya ce jami’an lafiya na daga ƙungiyar Houthi da ke iko da babban birnin na Yemen sun ce an garzaya da waɗanda suka ji raunuka da kuma waɗanda suka mutu zuwa asibiti a Bab-al-Yemen ɗin da ke tsakiyar birnin.

Hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yanayi na ruɗani da kuma gawawwakin yara duk kwakkwance.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here