Majalisar Dokoki Ta Kasa Ta Umarci Sirika Da Ya Dakata Da Rushe Ofishin Hukumomin Jiragen Sama.

<a href="https://
Majalisar dokoki ta kasa ta umarci ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da ya dakatar da shirin rushe ofisoshin hukumar da ke Legas.

Umurnin na zuwa ne bayan yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da kungiyoyin ma’aikatan sifirin jiragen sama suka shiga wanda ya janyo katsewar ayyukan jiragen a fadin kasar.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Disambar 2022, Sirika, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na rusa wasu ofisoshin hukumar dake Legas.

Ministan ya bayyana cewa za a bunkasa gine-ginen zuwa filin jirgin sama, yana mai jaddada cewa hakan zai taka rawa matuka ga daukacin masana'antar sufurin jiragen sama.

Sai dai a wata wasika da suka hada hannu da magatakaddan kwamitocin harkokin sufurin jiragen sama, Sanata Abiodun Olujumi da Nnolim Nnaji a ranar Laraba, sun bayyana damuwarsu kan yawaitar ayyukan masana’antu da kuma katsewar da ma’aikatan jirgin ke yi a kasar.

Sun yi nuni da cewa mafi yawan al’amuran da ke haddasa tada zaune tsaye ba sabon abu ba ne, kuma suna mamakin dalilin da ya sa suka ci gaba, suk da cewa wasu daga cikinsu an shafe shekaru ana takaddama akan su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here