Majalisar Dattawa ta tabbatar da Opeyemi a matsayin shugaban hukumar fansho ta ƙasa, tare da Hafiz Kawu da wasu uku a matsayin kwamishinoni

Barau Barau 1

Majalisar Dattawa ta amince da naɗin Opeyemi Agbaje a matsayin sabon shugaban hukumar kula da fansho ta ƙasa (PenCom) a zaman ta na ranar Talata.

Haka kuma majalisar ta tabbatar da nadin wasu mutane huɗu da za su kasance kwamishinoni a hukumar.

Wannan amincewar ta biyo bayan gabatar da jerin sunayen waɗanda aka zaɓa a zaman majalisar da mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya jagoranta.

Sanata Barau ya karanta sunayen Agbaje da sauran kwamishinonin da za su kasance a sabon kwamitin gudanarwar hukumar PenCom.

Daga cikin waɗanda aka tabbatar da nadinsu akwai Hafiz Mohammed Kawu, kwamishina mai kula da sashen fasaha daga yankin arewa maso yamma; Samuel Chigizie Nwandu, mai kula da sashen bincike daga kudu maso gabas; Charles Efe Sylvester Emukowate, mai kula da sashen kuɗi daga kudu maso kudu; da kuma Bello Abubakar Malabu, mai kula da sashen gudanarwa daga arewa maso gabas.

Shugaban kwamitin majalisar Dattawa kan kafa hukumomi da hidimar jama’a, Cyril Oluwole Fasuyi, ne ya gabatar da sunayen waɗanda aka zaɓa domin tantancewa da tabbatarwa.

Kafin wannan lokaci, Agbaje shi ne babban jami’in gudanarwa na kamfanin RTC Advisory Ltd, kuma ya yi karatun Banki da lauya, kuma ya taɓa zama shugaban asusun tsaron jihar Ogun.

Agbaje shahararre ne a matsayin marubucin ra’ayoyi da masani kan manufofi, kuma yana gabatar da shirinsa mai suna The Policy Council a talabijin, shi ma marubuci ne na littattafai da kuma malami a makarantar kasuwanci ta Jihar Legas.

Haka kuma, Hafiz Mohammed Kawu tsohon ɗan majalisar wakilai ne, inda ya wakilci mazabar Tarauni ta jihar Kano a majalisar wakilai ta tarayya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here