Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai kotun kolin kasar ta kebe hukunci a gaban wata kara da gwamnatin tarayya ta shigar a kan gwamnonin jihohin kasar nan 36 kan rashin da’a da ake yi a kananan hukumomin.
Kararrakin da Babban Lauyan Tarayya (AGF) da Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya shigar, na neman cikakken ‘yancin cin gashin kai ga daukacin kananan hukumomin kasar.
A cikin karar, gwamnatin tarayya ta yi batu ingantacce na musamman ga kotun da ta bayar da umarni, tare da haramta wa gwamnonin jihohi yin rusa shugabannin kananan hukumomi, ba bisa ka’ida ba.
Karin labari: “Ba faɗuwa na yi ba na rusuna ne don girmama dimokuraɗiyya” – Tinubu
Gwamnonin jihohin kasar 36 sun kai kara ne ta hannun babban Lauyan su.
Har ila yau karar na neman a ba da umarnin a ba su kudaden da ke hannun kananan hukumomi kai tsaye daga asusun tarayya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada wanda ya sabawa asusun hadin gwiwa da gwamnoni ke yi.
Gwamnatin tarayya ta kuma roki kotun koli da ta bada umarnin dakatar da gwamnoni ci gaba da kafa kwamitocin riko domin tafiyar da al’amuran kananan hukumomi wanda ya sabawa tsarin mulkin dimokuradiyya da tsarin mulki ya amince da shi.
Karin labari: Atiku ya jajantawa Shugaba Tinubu
Hakazalika ta nemi a ba da umarnin hana gwamnoni da wakilansu da masu fafutuka daga karbar ko kashewa ko kuma yin cuwa-cuwa da kudaden da aka fitar daga asusun tarayya domin amfanin kananan hukumomi idan ba a samar da tsarin kananan hukumomi na dimokuradiyya a jihohin ba.