Babbar Kotun jihar Kwara ta daure wasu dalibai uku tsawan shekaru biyar a gidan gyaran hali, bisa kama su da hada kai wajan yiwa yar uwar daya daga cikin su fyade.
Mai shara’a Adenike Akinpelu ya kamasu da life guda biyu wadan da suka hada da hada kai wajan aikata lefi sai kuma lefin fyade.
Wa dan da aka daure sune shine Omotosho Yahaya, da shekaru 23 wanda shine dan uwan wacce akayiwa fyaden, sai Mustapha Ahmed dan shekaru (23) da kuma Mustapha Ridwan dan shekara (22) wanda dukkkansu yan makarantar gaba da sakandare ne.
Alkalin ya kuma sa musu tarar dubu N50,000 ga kowan nan su, bayan daure.













































