Mutumin da ake zargi da kona Rebecca Cheptegei, ‘yar wasan tseren kasar Uganda, Dickson Ndiema, ya mutu.
A cewar hukumomin yankin, Ndiema, tsohon saurayin na Cheptegei, ya mutu ne a ranar Litinin sakamakon konewar da ya samu a harin da aka kai wa tsohon abokin aikin sa.
Ana zargin tsohon saurayin ne da watsawa Cheptegei fetir tare da banka mata wuta a lokacin da take komawa gidanta daga cocin da ke yammacin gundumar Trans Nzoia, Nairobi, ranar 1 ga Satumba.
‘Yar wasan mai shekaru 33 ta samu konewa a kashi 80 cikin 100 na jikinta kuma tana jinya a asibitin koyarwa na Moi da ke birnin Eldoret, inda ta rasu a ranar 5 ga Satumba.
Ndiema ya samu kuna a harin kuma an kwantar da shi a asibiti domin yi masa magani.
Cheptegei dai shahararriyar yar wasa ce, wacce ke zaune a Kenya, kuma ta wakilci Uganda a gasar Olympics ta Paris a 2024.
Yar wasan kuma ta kare a mataki na 44 a gasar tseren gudun fanfalaki na mata.
Ita ce fitacciyar ‘yar wasa ta uku da aka kashe a Kenya cikin shekaru uku da suka gabata.