Wata mummunar ambaliyar ruwa ta raba mutane sama da dubu (1,000) da muhallansu tare da salwantar da rayukan yara biyu a Kafanchan da kauyukan da ke yankin karamar hukumar Jema’a (LGA) ta jihar Kaduna.
Madam Christy Usman, mataimakiyar shugabar karamar hukumar Jema’a, ta bayyana hakan a wata ziyara da kwamitin tantance tasirin ambaliyar ruwa na jihar Kaduna ya kai wa al’ummar da abin ya shafa a kudancin Kaduna a ranar Litinin.
Ta ce, ambaliyar ruwan da ta afkawa sassan garin Kafanchan, Jagindi, Atuku, Aso da Bade, ta kuma lalata gonaki, inda amfanin gonaki na miliyoyin naira ya tafi.













































