Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatan jinya 2 da majinyata da dama a wata cibiyar kiwon lafiya a matakin farko da ke Kuyello a karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.
Wani dan banga mai suna Musa Alhassan, ya ce ‘yan bindigar sun far wa makarantar sakandaren gwamnati da ke kusa da wajen, inda suka isa da misalin karfe 9:00 na safiyar ranar Litinin.
“Lokacin da ‘yan fashin suka iske makarantar babu kowa, sai suka mayar da hankalinsu ga cibiyar kula da lafiya da ke kusa. ‘Yan fashin sun zo makarantar ne da misalin karfe 9:00 na safe, suna tambayar daliban, amma da suka fahimci makarantar babu kowa, sai suka je cibiyar kiwon lafiya suka fara garkuwa da mutane,” inji shi.
“’Yan bindigan da ke neman sace daliban, sai suka yi garkuwa da ma’aikatan jinya mata biyu da wasu marasa lafiya da dama, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba. Har yanzu ba a san ainihin adadin majinyatan da aka sace ba,” inji shi.
“’Yan bindigar sun zo ne a cibiyar kula da lafiya dauke da bindigogi da adduna. Sun fara fitar da mutane daga asibiti, kuma ba mu iya yin wani abu don hana su ba.”
Har yanzu dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna bai mayar da martani game da lamarin ba.